Connect with us

News

Bikin Sallah: Ta Ja Hankali Jama’a Kan Shirin Miyagu Na Dasa Bama-Bamai A Lokacin Sallah Karama Inji DSS

Published

on

Daga maryam bashir musa 

 

 

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bankado wani shiri da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kulla da nufin kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa da sauran wuraren da jama’a ke yawan zuwa kamar wuraren ibada da shakatawa, musamman a lokutan bukukuwan Sallah.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa makasudin kungiyar ta’addancin shi ne cimma wasu muradu na son kai tare da haifar da fargaba a tsakanin ‘yan kasa.

Advertisement

Wani bangare na sanarwar ya ce, “Ma’aikatar tsaro ta farin kaya ta cikin gida na jawo hankalin jama’a kan shirin ‘yan ta’adda na mayar da kasar shekarun baya wajen dana Bama-bamai a sassan kasar.

“Don haka, an umurci mazauna kasar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum sannan su sa ido da kai rahoto ga jami’an tsaro kan duk wani motsi da basu gamsu da shi ba.”

Shugaban Hukumar DSS, Alhaji Yusuf Magaji Bichi, ya yi fatan gudanar da bukukuwan ranar ma’aikata da bukukuwan Sallah cikin lumana da alkairi ba tare da wani cikas ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending