Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Lukaku, de Jong, Lewin, Coutinho, da Adeyemi
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku ba shi da sha’awar komawa AC Milan ko Newcastle a kakar wasa ta bana, duk da cewa dan wasan mai shekaru 28 ya kara nuna takaicin rashin samun dama a Chelsea. (Evening Standard)
Barcelona za ta saurari amsa a kan makudan kudin da sanya kan dan wasanta na tsakiya dan Netherlands Frenkie de Jong. Ana alakanta Manchester United da dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa. Erik ten Hag, wanda ya horar da De Jong a Ajax ne zai maye gurbin kocin kungiyar (Sport Spanish)
Shi kuwa Ten Hag, ya gano ‘yan wasa takwas da zai amince da su idan ya zama kocin United. Dan kasar Holland din mai shekara 52, yana fatan sayen dan wasan baya na bangaren hagu don taimakawa dan kasar Ingila Harry Maguire, mai shekara 29, kuma yana auna ko dan wasan Ingila Marcus Rashford zai iya kare lambarsa a kungiyar. (Telegraph)
Newcastle na zawarcin dan wasan gaban Benfica Darwin Nunez, mai shekara 22 dan kasar Uruguay da ake alakanta shi da Manchester United da Liverpool, a kokarin da suke yi na karfafa yan wasansu. Dan wasan Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 25, da kuma dan wasan Bayer Leverkusen na Jamhuriyar Czech, Patrick Schick, mai shekara 26, wya wasan da kungiyar ke bibiya {Mirror)
Kocin Tottenham Antonio Conte na son karfafa ‘yan wasansa wajen sayen dan wasan tsakiya na Southampton da Ingila James Ward-Prowse, mai shekara 27, da kuma dan wasan baya na Brighton da Spain Marc Cucurella, mai shekara 23. (Fichajes).
Barcelona ta gaya wa Aston Villa cewa tana da har zuwa karshen watan Mayu don yanke shawara ko tana son siyan dan wasan Brazil Philippe Coutinho mai shekara 29 a kan kwantiragi na dindindin a bazara. (Sports)
Manchester United ta gaza a yunkurin da take yi na daukar dan wasan gaban Red Bull Salzburg Karim Adeyemi, inda dan kasar Jamus din mai shekara 20 ke shirin komawa Bundesliga. (Patrick Berger)
Chelsea na son dauko dan wasan bayan Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 20, daga RB Leipzig, yayin da ake sa ran dan kasar Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 29, da kuma Dane Andreas Christensen mai shekara 26 za su koma Real Madrid da Barcelona. (Goal)
Arsenal na shirin zawarcin dan wasan baya na Bologna Aaron Hickey, mai shekara 19. Kocin Gunners Mikel Arteta na son kara karfin bayansa.(Goal)
Inter Milan ta shirya sayar da Stefan de Vrij kan fan miliyan 15 a wannan bazarar. Yanzu haka Tottenham, da Aston Villa da Newcastle na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan na Netherlands mai shekara 30. (Football Insider)
Arsenal za ta yi yunkurin karshe na kulla yarjejeniya da dan wasan Ingila Eddie Nketiah, mai shekara 22, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen watan Yuni, inda kungiyoyi a Ingila, da Faransa da Jamus ke zawarcinsa.(Mail)
Lazio na son rage farashin dan wasan tsakiyar Serbia Sergej Milinkovic-Savic zuwa kusan Yuro miliyan 80, yayin da Manchester United da Paris St-Germain ke zawarcinsa (Calciomercato)
Newcastle na fuskantar hamayya daga Paris St-Germain a yunkurin dauko dan wasan AC Milan na Portugal Rafael Leao, mai shekara 22. (La Repubblica)
