Connect with us

Politics

Ana cikin rashin tabbas a jam’iyyar APC

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

 

Kwanaki biyu a gudanar da zaɓen fitar da gwani domin tantace mutumin da zai yi takarar shugaban kasa a APC, rahoton kwamitin tantace masu takara har yanzu bai kammalu ba.

Najeriya ta haramta cin naman daji kan kyandar biri

Advertisement

Wannan na sake tada hankali tsakanin masu neman kujerar shugaban kasa da magoya-bayansu.

Kwamitin da ya tantace masu neman takarar, karkashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar, Cif John Odigie-Oyegun, ya tantace ‘yan takara 23 a ranar Talata a Abuja.

Tun bayan kammala tantacewar, ake cikin yanayi na ɗar-ɗar tsakanin masu takarar da magoya-baya kan abin da zai iya biyo baya a sakamakon tantacewar.

Sannan akwai rahotanni da ke cewa kwamitin ya karɓi korafi kan jagoran jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Wannan yanayi na rashin tabbas da ake ciki a APC ya zo daidai da kunnowar sabuwar ɓaraka tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar kan mutumin da zai gaji shugaba Buhari a 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending