Connect with us

News

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tace bata karbi sunan kowane dan takarar gwamna ba daga jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tace bata karbi sunan kowane dan takarar gwamna ba daga jam’iyyar PDP a jihar Kano.

DSS ta kama wani babban kwamandan ISWAP a Kano

Shugaban hukumar Farfesa Risk uwa ko Arabu Shehu ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Advertisement

 

 

Wannan na zuwane bayan yan takarar bangarori biyu na PDP a Kano sun fitar da hotunansu dauke da takaddar dake nuna sune halastattun yan takarar Gwamana a jam’iyyar a lahadinnan.

 

 

Bangaren PDP karkashin shugabancin Wada Sagagi da suka zabi Muhammad Sani Abacha da bangaren Aminu Wali da suka Zabi Sadiq Wali dukkaninsu na Ikirarin sune keda halastattun yan takara da zasu tsaya kujerar gwamnna a kakar zabe mai zuwa ta 2023.

Advertisement

 

To sai dai hukumar zaben mai zaman kanta ta bakin shugabanta na Kano tace har yanzu basu karbi sunan kowanne dan takarar gwamna daga jam’iyyu ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending