News
Wahalar man fetur tana ƙara ta’azzara a cikin garin Kano
Wahalar man fetur tana ƙara ta’azzara a cikin garin Kano
Daga Muhammad zahradd
Tun a ranakun ƙarshen makon nan ne dai wasu daga cikin gidajen mai suka fara rufe gidajen nasu, wasu kuma suka mayar da bayar da man nasu ta hanyar amfani da inji guda ɗaya tal.
Duk da cewa wasu daga cikin manyan gidajen man irin su Aliko da AA Rano suna ƙoƙarin bayan da man fiye da sauran, to amma a yau dai abin ya fara ƙamari ta yadda da yawa daga cikin gidajen man da ke birnin Kano suke a rufe, wasu kuma suke bayarwa da kai ɗaya.
Akwai dai mummunan raɗe-raɗin cewa lallai za a yi ƙarin, inda wasu rahotanni suke tabbatar da cewa za a iya ninka kuɗin man fetur daga nan zuwa watan Fabarairun wannan sabuwar shekarar.
Zuwa yanzu dai al’umma sun fara kokawa sosai saboda tsananin tsadar rayuwa da ƙunci da al’umma suka tsinci kansu a ciki.