News
Ƴan fashin daji sun kai hari Zariya sun kuma kashe mutum 4
Daga Muhammad zahraddin
Yan fashin daji sun kai hari kan unguwar Kofar Kona a Zariya ta Jihar Kaduna, inda su ka kashe mutum 4 su ka kuma ji wa da dama rauni.
Majiyoyi sun baiyanawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa ƴan ta’addan sun shiga unguwar a ranar Litinin da misalin ƙarfe 10 na dare, in da su ka riƙa harbi kan me-uwa-da-wabi.
An ce bayan harbe-harben, yan bindigar sun kaɗa wani garken shanu cikin jeji.
Jaridar ta ce wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce mazauna unguwar sun yi ta kiran lambar ƴan sanda amma ba a amsa kiran nasu ba.
“mun yi ta kiran lambobin kar-ta-kwana na ƴan sanda amma ba amsa. Sai bayan ma yan bindigar sun ci karensu ba babbaka sannan yan sandan su ka zo.
“Wajen mutum 24 a ka garzaya da su asibitin Gambo Sawaba can a Ƙofar Gayan, in da 4 su ka rasu sakamakon harbin da a ka yi musu da yawa a jikunan su.
“Sun kuma tafi da garken shanu na wasu Fulani sabbin zuwa a yankin,” in ji shi.
Jaridar ta ƙara da cewa Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Kaduna, Mohammed Jalige bai daga wayar da ta yi masa ba har zuwa lokacin da ta wallafa labarin.