News
Gwamnatin Taliban za ta fara zane waɗanda su ka makara zuwa Masallacin Juma’a a Afghanistan
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnatin Taliban, a ƙasar Afghanistan ta sanar da wata sabuwar doka da ta shafi dukkan al’ummar kasar.
Dokar ta baiyana cewar, da ga yanzu duk wanda ya makara bai je masallacin Juma’a ba har a ka soma Huɗuba, to za a yi masa bulala 25.
Dokar ta ce hukuncin babu babba, babu yaro, in da gwamnatin ta ce “saboda haka hukumomin Gwamnatin Taliban su ke kira ga dukkan al’ummar ƙasar Afghanistan da su kiyaye wannan doka, wajen zuwa Masallacin Juma’a akan kari.”
Gwamnatin ta baiyana cewar dokar za ta fara ne daga gobe Juma’a, shi ya sa ma a ka shiga kasuwanni ana sanar da jama’a dokar.
A gefe guda kuma, Gwamnatin ta samar da isassun bulalai ga dukkan jami’an tsaro da za su bi layi-layo don hukunta masu kunnen ƙashi.