Sports
Kotu ta bada belin ɗan bayan Man City, Mendy
Daga Muhammad zahraddin
Ɗan bayan Manchester City, Benjamin Mendy, ya shaƙi iskar ƴanci bayan da kotu ta bada belin sa a jiya Juma’a bayan an kawo ɗan wasan kotun da ga gidan yari.
Tun a watan Agusta ne dai a ke tsare da Mendy, ɗan ƙasar Faransa, bayan da a ke tuhumar shi da laifuka bakwai na fyaɗe da kuma laifi ɗaya na cin zarafi.
Ana tuhumar Mendy da aikata waɗannan laifuka a kan mata biyar, inda lamarin ya faru tsakanin watan Oktoban 2020 da Agustan 2021.
Sai dai kuma a zaman kotun na jiya Juma’a a ka baiwa Mendy, ɗan shekara 27 beli.
A wannan watan ya kamata a fara shari’ar, amma kuma kotun ta ɗaga zuwa watan Yuni, ko ma sama da haka.
A watan Disamba ne dai a ka rawaito cewa an ɗauke Mendy da ga gidan yari na HMP Altcourse da ke Liverpool zuwa gidan yari na Strangeways da ke garin Manchester.
Tuni dai Man City ɗin ta dakatar da Mendy tun sanda a ka fara tuhumar ta sa a watan Agusta.