Sports
AFCON 2021: Nijeriya ta doke Masar 1-0
Daga kabiru basiru fulatan
Tawogar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya mai suna Super Eagles ta doke takwararta ta Masar, wacce a ka fi sani da Egypt, da ci ɗaya mai ban haushi a gasar cin kofin kwallon ƙafa na Afirka na 2021.
Tun a minti na 30 ne dai ɗan wasan gaban Super Eagles ɗin, Kelechi Ihenacho ya jefa ƙwallon a ragar tawogar ƙwallon ƙafar Masar, wacce a ke kira ‘The Pharoahs’ a karawa ta farko a rukunin D.