News
Ahmed Musa ya baiwa Masallacin Juma’a gudunmawar dalar amurka 1,500
Daga kabiru basiru fulatan
Kaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya bayar da gudummawar dalar Amurka 1,500 ga wani masallaci a garin Garoua ranar Juma’a bayan kammala sallar Juma’a.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa Masallacin, wanda ke kusa da sansanin Eagles ɗin, (Hotel Le Ribadu) da ke Garoua, shi ne inda ‘yan wasa musulmin da ke cikin tawagar Nijeriya ke yin salloli biyar a kullum tun lokacin da suka isa yankin na arewacin Kamaru a ranar 5 ga watan Janairu.
Ana sa ran yin hakan zai taimaka wa malamai wajen kammala ginin Masallacin da ake ci gaba da yi.
A cewar wani jami’in tawogar, Musa, wanda ya buga wasa ɗaya a gasar bayan ya shigo a ɗan canji, ya kasance a ransa ya taimaka wajen gina masallacin tun da ya fara sallah a wurin.
“Kawai wani yunƙuri ne na godiya ga Hukumar Masallacin,” in ji jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunan sa.
Musa zai yi ƙoƙarin ya ga ya samu buga wasansa na biyu a gasar da Tunisia a wasan zagaye na 16 a filin wasa na Roumde Adjia da ke Garoua ranar Lahadi.