News
Ni ba dan siyasa ba ne, kaddara ce ta sa na zama gwamna – Zulum
Yasir sani Abdullahi
Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya Babagana Umara Zulum, ya ce shi ba dan siyasa ba ne, ƙaddara ce ta shigar da shi siyasa.
Zulum ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da jaridar Daily Trust ta shirya a Abuja wanda aka yi wa take “siyasa, tattalin arziki da tsaro”.
An shirya taron ne gabanin zaben 2023 domin tattaunawa kan makomar Najeriya, kuma ya samu halartar manyan baki kamar su tsohon shugaban kasar na mulkin soji Janar Abdulsalmi Abubakar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, da Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da kuma shi kansa Zulum da dai sauransu.
“Duk da cewa ni ne gwamnan Borno a yanzu, tsautsayi ne ya sa na zama, kuma ba wai cin dunduniyar ‘yan siyasa nake ba domin zan bar kujerar da nake a nan gaba. A yanzu da nake gabanku, kuma muke tunkarar 2023, kalubalen da yake gabanmu ba na wane ne za a zaɓa ba a matsayin kaza ba, a’a kalubalen shi ne wane ne ya cancanci matsayi kaza.
Zai yiwu da yawanku sun ɗara ni shekaru, amma ba ni da burin riƙe wani mukami sama da wanda nake rike da shi a yau, sai dai idan kaddara ce Allah Ya rubuta mani. Ba za mu cimma gaci ba har sai mun ajiye bambanci a gefe mun nemi wadanda suka cancanta, shi ne za mu iya samun shugabanni da suka dace”.