Connect with us

News

Fursunoni ‘970 suke yin digiri a gidanjen yarin Najeriya’

Published

on

122749521 3d2a7939 65af 4059 b85a 00f82e05b705.jpg
Spread the love
    1. Daga muhammad muhammad zahraddin Shugaban gidajen yarin Najeriya Halliru Nababaya ce akwai fursunoni ‘970 da suke yin karatun digiri a gidajen yari daban-daban na kasar’.

      Shugaban ya bayyana haka ne a Abuja ranar Juma’a inda yace fursunonin na karatun ne a jami’ar karatu daga nesa ta NOUN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

      “Wadan nan daban suke daga cikin fursunonin da wadanda suka zana jarrabawar WAEC da NECO kuma suka samu sakamako mai kyau,” in ji shi.

      Ya ce lokacin za a ce zayuwar mutum ta zo karshe domin an kai shi gidan yari ta wuce, yana cewa hukumar ta shirya domin bai wa fursunoni horo gabanin mayar da su cikin al’umma domin su zama wadanda al’umma za ta amfana da su a nan gaba.

      Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *