News
Kar ku zagi ko cin mutuncin Tinubu, Osinbajo ya gargaɗi magoya bayansa
Daga kabiru basiru fulatan
A yayin da fafatawar samun tikitin takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ke ɗaukar zafi, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gargaɗi magoya bayan sa kan zagi ko cin mutuncin jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, kuma tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Osinbajo ya taba zama babban lauya kuma kwamishinan shari’a na Legas a karkashin mulkin Tinubu.
A halin yanzu dai dukka su biyun na harin tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2023, wanda ya janyo cece-kuce tsakanin magoya bayansu.
Wasu magoya bayan Tinubu sun zargi Osinbajo da rashin goyon bayan yunkurin takarar shugaban kasa na mai gidan nasa duk da irin tagomashin da ya yi masa a siyasance.
Majiyoyi na kusa da mataimakin shugaban ƙasan sun ce Osinbajo ba ya goyon bayan duk wani wanda ke zagin Tinubu, don haka ya gargadi magoya bayansa: “Ko da magoya bayansa za su zagi mahaifiyata, kada ku rama. Ban ga dalilin da za a zage shi ko a tozarta shi ba”.
Har ila yau, majiyoyi sun bayyana cewa babban katangar goyon bayan Osinbajo shine sarakunan arewa, wadanda suke ganin Osinbajo ya nuna tsantsar biyayya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Baya ga sarakuna, an ce gwamnoni hudu ne na Arewa, biyu daga Arewa maso Yamma, biyu kuma daga Arewa ta Tsakiya, su ma an ce su ne za su tsaya takarar mataimakin shugaban kasa. Amma an ce Tinubu ya fi shahara a Arewa.