Connect with us

News

Ƙawata gada: PDP ta yi kira ga EFCC da ICPC da su binciki Ganduje kan kashe sama da Naira miliyan 500 wajen gyaran gada

Published

on

FB IMG 16434786415437687
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Babbar Jam’iyar adawa ta PDP a Jihar Kano ta yi kira ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da su binciki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sakamakon kashe Naira Miliyan 525 wajen ƙawata gadar ƙasa a jihar.

Jaridar indaranka ta rawaito cewa Majalisar Zartsawar jihar ce ta sanar da kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗe wajen yi wa gadar ƙasa ta Tijjani Hashim da ke kan titin Katsina ado da duwatsu na gida Nijeriya.

A wata sanarwa da Shugaban PDP ɗin na Jiha, Shehu Wada Sagagi ya sanyawa hannu kuma Yarabawa manema labarai a yau Asabar, jam’iyar ta koka da tsananin mamaki, matakin da Ganduje ya ɗauka na kashe sama da naira miliyan dari biyar wajen kawata gadar.

Advertisement

Sagagi ya ce ya na da kyau jam’iyar PDP ta jawo hankalin al’ummar Kano cewa kuɗaɗen da a ka amince da su don ƙawata gadar ta Kofar Ruwa almubazzaranci ne ga dukiyar al’ummar Jihar Kano.

Duk da cewa aikin yana da tsada sosai, Amma suna sane da Cewa an fara aiwatar da aikin da makonni kafin daga bisani Majalisar Zartaswar ta amince da fidda kuɗin, wanda baya cikin kasafin kudi na shekarar 2021 ko 2022.

In ji Sagagi, wannan laifi ne da zai iya janyo wa a iya tsige gwamnan, da a ce Kano tana da jajirtacciyar majalisar dokoki.

Advertisement

“Muna kira ga ’yan kungiyoyin farar hula da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC da ICPC da su binciki wannan ta’asa ta rashin gaskiya da rikon amana”. Inji Sagagi

A bayyane ya ke cewa gwamnan yana kan kashe kashen kudi domin kara durkusar da tattalin arzikin jihar Kano kafin cikar wa’adinsa na biyu don mayar da Kano baya.

“A matsayinmu na jam’iyyar adawa kuma ’yan jihar Kano nagari, mun yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da yin kira ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da kungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da wannan aiki domin kuwa Zai kawowa tattalin arzikin Jihar Kano Koma baya.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *