Sports
Kasuwar ‘yan ƙwallo: Makomar Militao, Silva, Zaniolo, Pochettino, Dybala, Keane, Saliba
Daga
muhammad muhamad zahraddin
Kocin Chelsea Thomas Tuchel na zawarcin ɗan wasan Real Madrid mai shekara 24, Eder Militao, domin maye gurbin German Antonio Rudiger. (AS – in Spanish)
Manchester City na tattaunawa da mai tsaron bayan Portugal Bernardo Silva kan yarjejeniyar mai tsawo duk da cewa kwantiraginsa sai shekara ta 2025 zai kare. (Times, subscription required)
Manchester United na fatan kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino ya koma horar da ‘yan wasanta a sabuwar kaka. (Mirror)
Pochettino mai 49 ɗan Argentina an ce ya gaji da sukar da yake fama da ita a kungiyarsa ta Faransa a yanzu don haka ba zai wuce wannan kakar yana mata aiki ba. (Footmercato – in French)
Shugaban Lyon Jean-Michel Aulas ya ce kungiyar za ta yi duk mai yiwuwa domin sayo dan wasan Faransa da ke taka leda Arsenal Alexandre Lacazette. (Sun)
Tottenham da Juventus sun kwaɗaitu da sayo ɗan wasan Roma mai shekara 22 Nicolo Zaniolo. (Calciomercato – in Italian)
Liverpool, Chelsea, Arsenal, Manchester City, Tottenham da Manchester United an ba su damar gabatar da tayinsu kan ɗan wasan Juventus Paulo Dybala bayan tattaunawar da ake yi da shi kan tsawaita kwantiraginsa ta rushe. (90min)
Sunderland na shirya tuntubar Roy Keane kan komawa kungiyar da horas da ‘yan wasanta. A shekara ta 2008 kocin mai shekara 50 yanzu ya bar kungiyar bayan daga mata kofi a 2007. (Mail)
Zakarun Italiya Inter Milan da abokan hamayyarsu AC Milan za su shiga karawa da Real Madrid a kokarin saye ɗan wasan Arsenal William Saliba wanda ke zaman aro a Marseille. (Calciomercato – in Italian)
Real Madrid na duba yiwuwar sake sayo Sergio Reguilon daga Tottenham a sabuwar kaka. (ABC – in Spanish)
Ana cewaBarcelona ta gano Manchester United da Juventus na kokarin ɗauke Ousmane Dembele, mai shekara 24, idan kwantiraginsa ya kare. (Sport – in Spanish)
Kungiyar Wayne Rooney Derby County mai fama da matsalar kudi ta amin ce da cinikin £600,000 da Aston Villa ta gabatar mata kan ɗan wasanta mai shekara 16 Omari Kellyman. (Sun)
Kungiyar Faransa da ke buga Ligue 1 Lille ta yi watsi da takin saye tsohon ɗan wasan tsakiya Jack Wilshire, wanda ya kasance ba shi da kungiya bayan baro Bournemouth a watan Mayu. (L’Equipe, via Metro)
Ana zawarcin Darragh Lenihanh na Blackburn Rovers a kulob din New York Red Bulls da ke Amurka wadda ta shirya zuba kudi domin sayo shi. (Football Insider)