News
Yadda ƙarancin man fetur ya jefa jama’a mawuyacin hali a Najeriya
Daga muhmmad muhmmad zahraddin
Jihohin Najeriya da dama sun shiga wannan makon da matsananciyar matsalar man fetur, wadda daman tun bayan sati biyu da suka gabata kasar ke cikin wannan matsala.
Bayan kwanaki da fara fuskantar ƙarancin man sai kuma aka fara samun wani gurbataccen man fetur wanda ya ringa lalata abubuwan hawa.
A dalilin samun wannan matsala hukumomi suka bayar da umarnin dakatar da sayar da man , har ma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin cewa lallai sai waɗanda suka shigar da man kasar sun yi bayani, yana mai bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare ‘yan kasar daga duk wani abu da za a samar wanda zai cutar da su.
Wannan matsala ta karancin man dai ana ganin ta haifar da gagarumin koma-baya ga harkokin tattalin arzki na jama’a da ma gwamnati kuma za ta ci gaba da hakan har zuwa lokacin da za a shawo kanta.
Halin da ‘yan kasa suka shiga
Jama’a sun wayi gari a ranar Litinin din nan 14 ga watan Fabrairu 2022, cikin tsananin wahalar man fetur din fiye da sauran kwanakin da suka gabata, inda wasu gidajen mai suka kasance a rufe,’yan kadan din da suke sayarwa kuma wasu suka ƙara farashi a wasu jihohin Najeriya.
A Abuja babban birnin tarayyar ƙasar, sakamakon karancin man kasancewar wasu gidajen man ba sa sayarwa, ma’aikata da sauran jama’a sun gamu da tsananin wahala ta neman ababan hawan da za su kai su wuraren aiki da sauran hada-hada ta yau da kullum.
Hakan ne ya sa ababan hawan da ake da su suka yi karanci matuka, abin da ya sa aka samu karin farashi na zirga-zirga musamman a cikin birnin na Abuja.
Wasu ma’aikata da sauran jama’a kuwa sun riƙa takawa da kafa zuwa wuraren ayyukansu, inda ya kasance babu nisa sosai, amma ga waɗanda wurarensu ke da nisa sai dai su haƙura bayan shafe sa’o’i da dama ba su samu abun hawa ba.
Yadda lamarin ya kasance a Kano
Can ma a jihar Kano babbar cibiyar kasuwanci ta arewacin kasar, matsalar ta man fetur din ta tsananta a wannan rana, inda wasu gidajen man ba su bude ba, yan ƙalilan din da suka buɗe kuma wasu sun ƙara farashin `har zuwa naira 220 a kan lita daya daga naira 162 zuwa 165.
Wannan ya sa aka tashi da matsalar zirga-zirgar ababan hawa wajen kai jama’a wuraren harkokinsu, abin da ya sa tashin farashin kuɗin sufuri.
Wani direba da ke tuka motar haya daga Kano zuwa Abuja Muntari Nasir ya sheda wa BBC cewa, ” a dalilin sayen man da tsada, dole suma su ƙara farashin inda ya ce, ”inda kake ɗauka naira 2,000, sai ka ƙara zuwa naira 3,000 ko ma zuwa dubu 3,500.”
Ya kuma ce a sanadiyyar matsalar sun samu raguwar fasinja.
Abubuwan da suka janyo karancin
A tattaunawar da BBC ta yi da shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ta arewacin Najeriya, IPMAN Alhaji Bashir Dan-malam, ya ce ai daman ita matsalar man fetur idan ta faru a kwana ɗaya sai an ɗauki kusan kwana biyar ko sati ɗaya kafin a iya warware ta.
Ya ce to wannan matsala ta samu ne a dalilai biyu zuwa kuku.
Ya ce matsala ta farko ita ce ta ƙin sayar da man a manyan rumbunan adana man da ke Warri da Lagos da Patakwal da kuma Calabar.
Sai kuma matsalar motocin dakon man misali motar da za ta ɗauki man daga rumbun da ke Apapa zuwa inda ake buƙata, saboda an ce motocin su dakata da ɗaukar man mai kyau da kuma wanda ake ganin ba shi da kyau.
Shugaban ya ce wani abu kuma da aka saba gani shi ne, ”daman a karshen sati, Asabar da Lahadi a al’ada ana samun hutu, amma kuma duk da cewa NNPC ta ce a koma aiki awa 24, wannan ma ta taimaka wajen tsanantar ƙarancin saboda wasu ba za su samu damar zuwa aiki ba domin akwai masu zuwa ibada a ƙarshen sati.
Warware matsalar
Shugaban kungiyar dillalan ya ce ana sa ran raguwar matsalar a cikin satin nan inda ya ce, ”a yau Litinin 14 ga watan Fabrairu 2022, jihar Kano ta samu mota 154 ta man, wacce za a rarraba a jihohin Kano da Katsina da Jigawa da kuma Bauchi.
Ya kuma kara da cewa, ko a ranar Lahadi sun yi magana da hukumar NNPC inda ta bayar da umarnin a buɗe runbunan man da ke arewa misali na Suleja da Minna da sauransu da wadanda ke yankin arewa ta tsakiyar ƙasar, da na yankin kudu masu gabashin ƙasar domin samar da man.
A karshe dai ya ce suna sa ran a samu saukin matsalar zuwa kwana hudu.