News
Ƙarin farashin man dizel zai ƙara tsadar kayayyaki a ƙasar nan, IPMAN ta yi gargaɗi

Daga maryam bashir musa
Wani ƙusa a Kungiyar Dillalan Man Fetur mai Zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, Chinedu Anyaso ya yi gargaɗi cewa ƙarin farashin man dizel zai haifar da hauhawar farashin kayaiyakin masarufi a ƙasar nan.
Anyaso, wanda shi ne Shugaban masu harkar rumbunan man fetur (depot) na Enugu, ya baiyana hakan ne a yayin tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a Awka.
Ya baiyana cewa ƙarin farashin babbar matsala ce domin zai ƙara wa ƴan ƙasa raɗaɗin zafin rayuwa.
NAN ya rawaito cewa farashin man dizel ya tashi a makonni biyu da ga N400 zuwa N650 a Awka.
Sabo da rashin tsayayyar wutar lantarki a kasa, man dizel ne abin amfani a injina a manya-manyan guraren al’umma kamar su kamfanunuwa, otal-otal, masana’antu da sauran su.
Ya ce halin da a ke ciki ba mai dadi ba ne ga IPMAN da ma harkar kasuwanci a ƙasa baki ɗaya.