News
Rasha ta ce ta kammala kashin farko na yaki a Ukraine
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Hukumomin sojin Rasha sun ce sun kammala kashin farko na yakin da suke yi a Ukraine, yanzu kuma za su mayar da hankali ne ga yankin Donbas na gabashin kasar, wanda ya kunshi kasashe biyu da suka balle, wadanda ke bin tsarin Rasha.
Yankin ya kunshi Donetsk da Luhansk, wadanda ke hannun ‘yan aware masu samun goyon bayan Rasha tun 2014, wadanda kuma a hukumance suke da ‘yancin kansu a wajen Rasha, kafin wannan kutsen da ta fara a Ukraine.
Sai dai kuma a wurin jami’an kasashen Yamma, wannan sanawa na nuna cewa Moscow ta san cewa dabara ko nufinta na kafin ta kaddamar da yakin ya gaza.
A cikin wata daya da ya wuce, dakarun Rasha sun ci gagarumar nasara a wannan yanki, da kuma gefen kudanci wanda ya hada ta da Crimea, tsibirin da shi ma gwamnatin Rasha ta mamaye a 2014.
Manjo Janar Sergei Rudskoi ya ce Rasha ba ta daina kai hare-hare ba a sauran birane ba, wadanda suka hada da babban birnin Ukraine din Kyiv, amma wannan ba shi ne ainahin babbar manufarta ba.
Wadannan kalamai dai su ne alamu na farko da ke nuna cewa kila Moscow na takaita nufinta na yakin bayan wata daya da kaddamar da shi, inda ta kasa kama ko da wani babban birni daya na Ukraine, kuma hare-haren nata sun gamu da cikas na matsalar kayan aiki da kurakurai da kuma gagarumar turjiya ta Ukraine.

Amma dai duk da haka zuwa yanzu dakarun Rashar na nan a bakin daga, kuma cikin aiki a kusan dukkanin fadin Ukraine.
Kuma yawancin ‘yan Ukraine na kokawa kan matsanancin halin da suke ciki, ganin irin asarar rayukan da ake yi a yakin na kara fitowa fili.
A yanzu ne cikakkun bayanai ke fitowa fili na yawan mutanen da suka rasu a harin da Rasha ta kai a makon da ya gabata a kan wani babban zauren taro da wasanni a birnin Mariupol da sojan Rashar suka yi wa kawanya.
Hare-haren da Rasha take kai wa ta sama ba kakkautawa sun hana aikin ceto da ake matukar bukata. Amma dai akwai kyakkyawan fatan cewa wasu mutane kusan dubu daya wadanda yawanci mata ne da kananan yara da ke boye a dakin karkashin kasa suna da kariya.

Hukumomi sun ce zuwa yanzu kusan mutum dari uku aka hallaka, a birnin kuma dauki-ba-dadin da ake tafkawa kan birnin na Mariupol na ci gaba da wanzuwa.
Magajin garin birnin ya ce an lalata birnin na kudu maso gabas sosai kuma za a dauki shekaru ba a iya gyara shi ba.
Birtaniya ta ce sojin Ukraine na sake kwato wasu garuruwa da kuma kare gabashin Kyiv.
A halin da ake ciki Shugaban Amurka Joe Biden na Poland inda yake kammala ziyararsa a Turai kan rikicin.
Tun da farko Turai da Amurka sun bayar da wata sanarwa ta babbar yarjejeniya da suka kulla ta samar da makamashin gas ga Turai domin rage dogaro da makamashin Rasha da Turai ke yi.
