Connect with us

News

AN TSIGE SHEIKH NURA KHALID DAGA LIMANCI SABO DA SUKAR GWAMNATI A HUƊUBAR JUMA’A

Published

on

 

Kwamitin Masallacin Appo Dake Abuja Ta Tsige Shaikh Nura Khalid (digital Imam) Daga Limancin Masallaci, Sabo da Caccakar Gwamnatin Buhari da Yayi Jiya A Huɗubar Juma’a, Akan Matsalar Tsaro Daya Addabi Al’ummar Ƙasar.

Malamin Dai Yayi Kira Ga Talakawan Najeriya akan Idan Har Gwamnati Bazata Iya Kare Rayukansu ba, to Karda Su Fito Ranar Zaɓe.

A cikin wani saƙo da shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau ya aika wa manema labarai, ya ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama’a, Suyiwa Gwamnati Bore.

Sanarwar ta ce: “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ƴan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.”

Ya Kuke kallon wannan Matakin, Shin Hakan Na Nuna Kwamitin Masallacin Sun damu da Al’ummar su kenan?

Advertisement

Ko kuma dai umurni ne daga Sama?
-Idrees Muhammad Katusha

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending