Connect with us

News

Mai ba wa Shugaba Buhari shawara kan tsaro Monguno ya ja kunnen El-Rufai

Published

on

Daga Kabiru basiru fulatan

Mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, manjo Janar Babagana Moguno ja kunnen Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai game da kalaman da ya ce gwamnan na yi kan harkokin tsaro.

Monguno ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen wata ganawa da shugaban kasa da hafsoshin tsaro a Abuja. “Gwamna Nasir El-Rufai ya yi magana kan hukumomin tsaron kasar nan yana cewa wai mun san ko su wane ne ‘yan ta’addan nan, da inda suke,” a cewarsa.

Monguno ya kara da cewa “wannan shi ne babban haɗarin, musamman idan ka fara maganar da ba ta dace ba, sai kai ta fadin abin da ba shi kenan ba”.

Bayan harin da aka kai kan jirgin kasa a watan Maris, Gwamna El-Rufai ya bukaci jami’an tsaro su kai hare-hare a maboyar ‘yan bindigar da ke dajin maimakon a jira su kai farmaki.

El-rufa’i ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaron sun san sansanonin ‘yan bindigar da lambobin wayarsu, inda ya jaddada bukatar kai hari kan ‘yan ta’addan.

Advertisement

Shugaba Buhari ya gana da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban a ranar Alhamis.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending