News
Masu zanga-zanga sun yi dafifi a ofishin Goodluck Jonathan, sun bukaci ya fito takara
Yasir sani abdullahi
Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa, wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a gaban ofishin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a Abuja suna neman ya sake tsayawa takarar mukamin shugaban kasar a zaben shekarar 2023.
Mutanen wadanda suka ce ‘ya’yan wata kungiya ce ta matasa, sun isa ofishin ne dauke da sakonni bisa takardu da ke kira ga tsohon shugaban ya fito ya tsaya takara.
Wasu takardun na dauke da hotunan Mista Jonathan inda suke cewa: “Sai ka tsaya takara Goodluck Jonathan”, “Muna bukatar ka ceto Najeriya”.
Kakakin kungiyar, Mayor Samuel, wanda shi ne mai kungiyar Youth Compatriots of Nigeria ya ce “Wadanda suka ce a mika musu mulki a 2015 cewa za su gyara kasarmu sun yaudare mu”.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
