News
Tsohon Shugaba Kibaki na Kenya ya mutu yana da shekara 90
Daga Muslim yunus Abdullahi
Tsohon Shugaba Mwai Kibaki na Kenya ya mutu, kamar yadda Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ya sanar cikin wata sanarwa.
Mista Kibaki ne shugaban kasar na uku tun bayan da kasar ta sami ‘yancin kai daga Birtaniya a 1963.
Shugaba Uhuru Kenyatta ya ayyana kwanakin zaman makoki a fadin kasar har zuwa ranar da za a binne tsohon shugaban kasar.
Ya kuma ce za a ba tsohon shugaba Kibaki dukkan karramawar da tsohon shugaban kasa ya kamata ya samu bayan mutuwarsa.
Akan haka ne za a sauko da tutocin kasar kasa-kasa a gida da kuma a dukkan ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje.
Mista Kibaki ya rike mukamin shugaban kasar Kenya daga 2002 zuwa 2012.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
