Connect with us

News

Iran da Saudiyya na sasantawa a Iraƙi

Published

on

Daga Kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

 

Rahotanni sun ce Saudiyya da Iran sun koma teburin tattaunawa da nufin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu da ke gaba da juna.

Advertisement

Kawo yanzu babu wani tabbaci a hukumance, amma wani shafin intanet na yada labarai na gwamnatin Iran ya ce an yi tattaunawar a Bagadaza.

Kasashen biyu na adawa da juna a wasu rikice-rikicen yankin ƙasashen Larabawa da kuma rikicin siyasa.

Advertisement

Sai dai sun fara tattaunawa a bara da nufin rage barazana a yankin.

Iran ta dakatar da tattaunawar a watan da ya gabata ba tare da bayar da wani dalili ba. Matakin ya biyo bayan hukuncin kisa da mahukuntan Saudiyya suka yi wa mutum 81 a rana daya – wanda aka ce rabinsu ‘yan Shi’a ne tsiraru.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending