Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mane, Savic, Romagnoli, Pogba, Pepe da Jesus

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Manchester City na sha’awar sayen dan wasan Leeds da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26, yayin da take neman maye gurbin dan wasan Brazil Fernandinho, mai shekara 37, wanda zai bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana bayan shekaru tara. (Mirror)

Paris St-Germain na shirin daukar dan wasan gaban Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane, mai shekara 30, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa ya ki amincewa da sabon kwantaragi. Kwantiragin Mane na yanzu zai kare ne a watan Yuni 2023. (Sport Bild)

Advertisement

Sabon kocin Manchester United Erik ten Hag ya saka dan wasan bayan Argentina Lisandro Martinez, mai shekara 24, cikin jerin ‘yan wasan da yake son kawowa Old Trafford a bazara. Martinez ya taimaka wa Ajax ta lashe gasar Dutch a 2021-22. (Telegraph)

A halin da ake ciki, United tana kuma sha’awar dan wasan Lazio dan kasar Serbia Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27, wanda ya zura kwallo 11 da taimakawa aka ci 11 a wasanni 36 da ya buga. (Calciomercato)

Advertisement

 

PSG da Juventus na ci gaba da neman dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 29, wanda kwantiraginsa zai kare a bazara. (Fabrizio Romano)

Advertisement

Chelsea na son dauko kyaftin din AC Milan kuma dan wasan bayan Italiya Alessio Romagnoli, mai shekara 27, a bazarar nan ba tare da ta biya kudi ba, sabod kwantiraginsa zai kare. (Mundo Deportivo)

Dan wasan Arsenal dan kasar Ivory Coast Nicolas Pepe, mai shekara 26 wanda ya koma kungiyar kan kudi fam miliyan 72 a shekarar 2019 ya ji takaicin rashin samun damar buga wasa a kungiyar, don haka zai iya kaura (Mirror)

Advertisement

Arsenal ta dage da zawarcin Gabriel Jesus

A halin da ake ciki, ana sa ran Gunners za ta kai tayin fan miliyan 35 don siyan dan wasan gaban Manchester City na Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 25, wanda ke shirin tafiya bayan zuwan Erling Haaland. (football.london)

Advertisement

Sannan shugabannin Arsenal suna tattaunawa kan ko za su sayar da dan wasan baya na Brazil Gabriel Magalhaes a bazara, tare da biyan fan miliyan 51 kan dan wasan mai shekara 24, wanda Juventus ke zawarcinsa. (Tuttosport)

Dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, mai shekara 22, da dan wasan gaba na Albania Armando Broja, mai shekara 20, za su koma Chelsea idan zamansu na aro a Crystal Palace da Southampton ya kare a karshen kakar wasa ta bana. (Fabrizio Romano)

Advertisement

 

Chelsea ta fara shirin dauko dan wasan bayan Sevilla na kasar Faransa Jules Kounde, mai shekara 23 (Goal)

Advertisement

Dan wasan tsakiya na Aston Villa da Scotland John McGinn, mai shekara 27, yana cikin jerin wadanda Tottenham za ta yi zawarci a bazara. (Telegraph)

Dan wasan Fulham da Kamaru Andre-Frank Zambo Anguissa, mai shekara 26, zai ci gaba da zama a Napoli a kakar wasa mai zuwa bayan ya koma kungiyar a matsayin aro na tsawon kaka a watan Agustan da ya gabata. (Football Italy)

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending