Connect with us

News

Zamu hukunta bola tinibu bisa kalaman da ya fada akan buhari

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

Shugaban jam,iyyar Apc na kasa Sanata Abdullahi adamu yace zasu iya hukunta jigo a jam,iyyar Apc wato tsohon gwamnan jahar Legos bola ahmad tinibu bisa wasu kalamai da ya fada akan shugaban kasa muhammadu bahari

Advertisement

A ranar Alhamis data gabata jaridar aminiya ta rawaito cewa tinubu yace shine gatan shugaban kasa bahari na danewa karagar Mulki a shekarar 2015 Kuma tinibun ya Kara da cewa da badan Shiba da bahari ba zai ci mulkiba

Tinubu ya bayyana hakan ne a masaukin shugaban kasa a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget din APC gabanin zaben fitar da gwani na jam’iyyar da za a gudanar a makon gobe.

Advertisement

Ya ce “bayan faduwa zabe har sau uku, Buhari ya yi koka yana mai cewa ba zai kara tsayawa takara ba, amma ni [Tinubu] na garzaya har Katsina na roki Buhari da ya sake tsayawa takara kuma zai yi nasara saboda ni da wasu za mu shige masa gaba.”

Wadannan kalamai dai sun janyo cece-kuce a fadin kasar, inda da dama ke zargin Tinubu da goranta wa Buhari da har wasu ke ganin ya kamanta kansa da Allah mai jibinta lamurra.

Advertisement

Sai dai da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja ranar Asabar, Adamu ya ce, “Muna iya hukunta shi [Tinubu] kan kalaman da ya yi wa Shugaban Kasa.

An ruwaito shugaban jam’iyyar yana cewa ba su ji dadin kalaman ba musamman daga Tinubu da ake kira jagoran jam’iyyar.

Advertisement

“Bai kamata ya kawo zancen abin da bai shafi Buhari ba, har ya ambaci sunansa, wanda mutum ne da muke ganin kimarsa a rayuwar jam’iyyarmu,” in ji shi.

Ya ce kuskure ne ya ambaci Buhari a wurin da ba ya nan.

Advertisement

Daga baya Tinubu ya fito ya ce ba a fahimci kalamansa ba ne, yana mai cewa yana matukar mutunta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma ba zai taba raina shi ba.

Amma Shugaban APCn ya bayyana kalaman na Tinubu a matsayin “kururuwa bayan yaki” yana mai cewa kamata ya yi ya je ya ba Buhari hakuri.

Advertisement

“Ni ina ganin Tinubu ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya yi kalaman,” in ji Abdullahi Adamu.

Shugaban na APC kuma ya ce dukkanin masu neman kujerar Shugaban Kasa mutum 23 za su yi takara a zaben fitar da gwani da jam’iyyar za ta gudanar a makon gobe, sabanin rahotannin da ke cewa an cire sunayen mutum saboda rashin cancanta

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending