Connect with us

News

Al-Shabab na tursasa wa manoma biyan haraji a Somaliya

Published

on

Al-shabab

Daga Khadija abdullahi muhmd

 

 

 

Haraji mai tsanani da ƙungiyar al-Qaeda mai ƙawance da al-Shabab ta ƙaƙaba wa mutane a wasu yankunan Somaliya ya sa manoma ba sa iya girbe amfanin gonarsu a yayin da ake fama da matsannacin fari.

Zai yi wuya INEC ta iya yi wa ƴan Najeriyar da ke son yin katin zaɓe rijista’

Advertisement

Za’a Yi Jigilar Maniyyata Aikin Hajjin Kaduna 2491 Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

 

Abdirahman Abdishakur Warsame, jakada na musamman ga shugaban ƙasar Hassan Sheikh Mohamud a kan batun farin, ya ce harajin na al-Shabab na tursasa wa manoma tserewa su bar gonakinsu da gidajensu.

 

Mr Warsame ya shaida wa shugaban ƙasar da shugabannin gundomomin ƙasar hakan ne a jiya Lahadi a wani taro da aka shafe kwana biyu ana yi.

 

Advertisement

Ya ce fiye da ƴan Somaliya miliyan bakwai ne fari ya shafa. Kuma mutum 250,000 daga cikinsu na fuskantar matsananciyar yunwa.

 

Al-Shabab na yawan amfani da yunwa da ake fama da ita a ƙasar don ƙara fito da kanta da kuma bayar da tallafi ga jama’a.

Source BBC

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending