Connect with us

News

Yan bindiga sun sace limamin coci da matarsa a Kwara

Published

on

Wasu rike da bindigogi

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

 

 

Wasu ‘yan bindiga sun sace Bishop na darikar Anglican, Rabarand Oluwaseun Aderogba da ke Jebba a Jihar Kwara ta Tsakiyar Najeriya tare da matarsa da dirabansa.

Advertisement

ajin Aiki: ASUU Ta Lashi Takobin Hukunta Jami’o’in Da Suka Bijire Mata

Gidan talbijin na Channels TV ya rawaito cewa an sace mutanen ne ranar Lahadi da maraice a kan hanyar Oyo/Ogbomoso da ke Jihar Oyo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da sace mutanen a wata sanarwa da ya fitar.

Ya kara da cewa wani mutum mai suna Rabarand Adekunle Adeluwa ne ya kai wa ‘yan sanda labarin sace takwaransa.

A cewar Osifeso, binciken farko ya nuna cewa motar limamin cocin ce ta samu matsala a yayin da suke tafiya daga Yewa da ke Jihar Ogun zuwa Jebba a Jihar Kwara.

Ya kara da cewa an bai wa mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan yankin umarnin gano da kuma ceto mutanen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending