Opinion
Haƙƙin gyaran Arewa yana hannun al’ummarta ba wai shugabanninta ba-kabiru basiru fulatan
Daga kabiru basiru fulatan
A haƙiƙanin gaskiya a yanzu babu wani yanayi da za mu jira sai wasu “shugabanni” sun zo sun yi mana wani aiki. Duk abin da muke so Arewa ta zama to mu ne za mu shata hakan kuma mu tashi haiƙan mu yi aikin cim ma wannan mafarkin. Kuma mai yiwuwa ne ƙwarai da gaske.
Obasanjo Ya Yi Direban Keke Napep Na Yini Daya
A baya muna da sarakuna, waɗanda su ne shugabanni. Amma tsarin da muke a kai a yanzu babu wasu mutane da aka ware waɗanda dole sai a cikinsu shugabanni za su fito, kamar yadda ake yi a lokacin sarakuna. Don haka duk waɗanda suke son zama shugabanni kawai layin za su bi.
To, masu ilimi, na zamani da na addini, a wannan yanki, ashe su ne za su iya tashi su haɗa kai su shata wa manufar da suke son ganin mun cim ma, ta kowace fuska, sannan mu bi hanyar samun shugabancin, duk wuyarsa, domin mu iya aiwatar da wannan ƙudurin.
Jiran sai “shugabanni”nmu na yanzu sun yi abin da mu muke ganin shi ya dace, ko kuma jiran su tunkari abin da mu muke ganin bala’i ne, ba lallai ya iya biya mana buƙata ba. Saboda akwai bambancin fahimta, da bambancin “generation” da bambancin aji da bambancin mafuskanta da sauransu.
Mu ya kamata mu tashi mu yi abin da ya kamata, kamar yadda yan bokonmu na farko, irin su Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sardauna da Sa’adu Zungur da Aminu Kano da su Abubakar Imam da sauransu suka yi aikin da muke cin gajiyar sa a yanzu.
Sai fa mun farka!
