News
Jama’a a Sudan na ci gaba da zaman ɗar-ɗar
Jama’a a Sudan na ci gaba da zaman ɗar-ɗar
Jama’a a Sudan na ci gaba da zaman dar-dar sakamakon yadda ake ci gaba da samun rikici tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar neman komawa mulkin dimukradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Gamin gambizar da aka yi tsakanin sojoji da farar hula don shugabancin kasar a 2019 bai yi nasara ba, bayan da sojoji suka tilastawa firaminista Abdallah Hamdok yin murabus a bara.
Lamarin ya kara jefa kasar cikin halin rashin tabbas.
Advertisements
