Connect with us

News

An Rufe Makarantu A Sudan Ta Kudu Saboda Yanayi Na Matsanancin Zafi

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

Yanayi na matsanancin zafi ya tilasta wa mahukuntan Sudan ta Kudu rufe makarantu a fadin kasar don kauce wa irin hadarrin da ke tattare da yanayin, duba da yadda ya ke ci gaba da ta’azzara.

Advertisement

Bayanai sun ce masana yanayi sun tabbatar da cewa nan da makonni masu zuwa kasar za ta tsinci kanta cikin tsananin zafin da bata taba ganin irin sa a tarihi ba.

Za A Sallami Akalla Daraktoci 8 Da Ke Aiki A CBN Bisa Wani Dalili Da Haryanzu Ba A Gama Fayyacewa Ba. 

Ma’aikatar Ilimi da ta lafiya sun yi hadin gwiwa wajen shawartar iyaye da su yawaita zubawa yaran su ruwa ajiki tare da killace su a gida ba tare da barinsu shiga rana ba.

Advertisement

Gwamnatin kasar ta yi barazanar karbe lasisin duk makarantar da aka samu a bude lokacin wannan tsananin zafi, sai dai kuma bata yi karin haske kan lokacin da za’a bude makarantun ba.

Masana yanayi sun alakantan tsananin zafin da karancin ruwan sama, sauyin yanayi da kuma fari da kasar ke fama da shi.

Advertisement

 

Fri

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending