Connect with us

News

Sama da mutane 100 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Kwalara a Kasar Sudan

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Ma’aikatar lafiya ta kasar Sudan ta sanar da cewa, barkewar cutar kwalara da zazzabin dengue a kasar Sudan da yaki ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 tun daga watan Agusta.

Ma’aikatar ta ce an samu adadin mutane 1,049 da suka kamu da cutar kwalara, 73 daga cikinsu sun mutu a birnin Khartoum na jihar Al-Jazira da ke kudu da Gedaref a yammacin kasar.

Advertisement

 

Jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar Gwamna a Jihar Bayelsa –Hukumar INEC

Khartoum na daya daga cikin manyan gurin  fadace-fadacen da ake gwabzawa  ya mamaye kasar tun watan Afrilu.

Advertisement

Dubban daruruwan mazauna babban birnin Khartoum sun yi gudun hijira zuwa yankunan Gedaref da Al-Jazira da aka kwantar da hankula,

Jihohi tara na Sudan sun sami rahoton bullar cutar zazzabin cizon sauro, inda 49 suka mutu daga jimillar mutane 3,316, in ji ma’aikatar.

Advertisement

Jihar Gedaref, mai makwabtaka da Habasha, ta ba da rahoton mutane 2,152 daga cikin wadanda suka kamu da cutar sannan 33 daga cikin wadanda suka kamu sun  mutu.

Tun kafin fadan ya barke a cikin watan Afrilu, tsarin kula da lafiya na Sudan ya yi kokarin shawo kan barkewar cutar da ke tare da damina a kasar da ke farawa a watan Yuni.

Advertisement

Rahoton ma’aikatar lafiya ta  ce kashi 70 cikin 100 na asibitocin da ke yankunan da yaki ya daidaita ba sa aiki.

 

Advertisement

 

Daily Trust 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending