Connect with us

News

Jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar Gwamna a Jihar Bayelsa –Hukumar INEC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamnan Bayelsa da Imo da aka yi wa gyaran fuska.

Bisa ga lissafin da aka yi wa gyaran fuska da hukumar ta wallafa a ranar Talata, ba a saka sunayen Timipre Sylva da abokin , Joshua Maciver na jam’iyyar APC  ba a zɓen jihar Bayelsa.

Advertisement

Me kuke tunanin ya sa mawaki Dauda Rarara caccakar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari?

Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony ne ta sanya hannu a jerin sunayen.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, an bar shafi na sunayen ɗan takarar Jam’iyyar APC da abokin takararsa tare da umarnin kotu a jiki.

Advertisement

Haka kuma a jihar Imo, hukumar ta haɗa da sunayen Uchechukwu Ishiodu a matsayin ɗan takarar gwamna da Ahumbe Chiazor a matsayin abokin takarar jam’iyyar Peoples Redemption Party a zaɓen jihar.

 

Advertisement

Ta ce bayan wallafar, an ba wa hukumar umarnin kotu game da tsayar da ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa.

 

Advertisement

An sabunta jerin sunayen ‘yan takara dangane da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na 2023 bisa ga umarnin kotu da hukumar ta bayar,” in ji Oriaran-Anthony.

 

Advertisement

 

A ranar 10 ga watan Oktoba ne babbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramta wa Sylva shiga zaɓen gwamnan jihar.

Advertisement

 

Mai shari’a Donatus Okorowo, a hukuncin da ya yanke, ya ce Sylva da aka rantsar da shi sau biyu kuma ya yi mulki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan jihar Bayelsa, zai saɓa wa kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima idan ya sake tsayawa takara.

Advertisement

A wani labarin kuma Me kuke tunanin ya sa mawaki Dauda Rarara caccakar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari?

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending