News
Kotun Kolin ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar.
Kotun Kolin ta tabbatar da hakan ne a hukuncin da ya zama na karshe da ta yanke a yau Alhamis a kan zaben shugaban Nijeriya wanda Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour ke kalubalanta.
Tawagar alkalai bakwai ce ta yanke hukuncin bayan yin nazari a kan hukunce-hukuncen da kotunan baya suka yanke.
Tun farko Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun nemi Kotun Kolin ta soke zaben Bola Tinubu wanda kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da nasararsa a matsayin shugaban kasa a zaben 2023.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
