News
Tsadar Rayuwa: An Samu Karancin Bai Wa Almajirai Sadakar Abincin A Azumi
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Wasu almajirai a jihar Kano sun bayyana yadda suka daina samun sadakar abinci a cikin wannan wata na azumi, sabanin shekarun baya kamar yadda Shirin Rayuwata na sashen Hausa na rediyon Faransa ya rawaito.
Haka kuma Almajiran sun ce ba sa samun abinci a lokacin bude-baki da kuma sahur.
An Rufe Makarantu A Sudan Ta Kudu Saboda Yanayi Na Matsanancin Zafi
Ana kallon wannan lamari na da nasaba da tsadar rayuwar da ake fama da ita a sassan Najeriya, yayin da ake ci gaba da kira ga mawadata da su kara kaimi wajen tallafa wa talakawa da abinci musamman a watan nan na azumi.
Yawon bara tsakanin yara da manya a jihohin arewacin Najeriya wata babbar matsalace data gagari jihohin da ke yankin tsawon shekaru.
Al’ummar Najeriya sun samu kansu cikin halin taskun rayuwa, tun bayan da mahukuntan kasar suka kara kudin wutar lantarki da farashin litar man fetur, abin da ya haddasa tsadar kayan masarufi da ma uwa uba kayan abinci.
