News
Wani mutum ya kona matarsa a jihar Ogun
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
‘Yan-sanda sun ce shi ma mijin ya rasu bayan an kama shiImage caption: ‘Yan-sanda sun ce shi ma mijin ya rasu bayan an kama shi
Abubuwan da suka haddasa tsadar takin zamani a Najeriya
Wani mutum a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, Ponle Adebanjo, ya kona matarsa, Lateefat, abin da ya kai ga mutuwarta saboda ta gudu ta bar shi a kan yawan dukanta da yake yi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a yankin Otun-Akute da ke jihar ta Ogun.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar , DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce, a ranar Asabar da daddare ne mijin ya bi matar zuwa wani gida da ta koma a unguwarsu, ya tarar da ita tana sallah, ya kwara mata fetur ya cinna mata wuta.
A sanarwara da kakakin ‘yan sandan ya fitar ya ce, ganin haka ya sa ita ma matar ta kama mijin nata ta rike don su kone tare, har sai da mutane suka zo aka shiga tsakani.
Kakakin ya ce bayan an garzaya da matar asitbiti ne likita ya tabbatar ta rasu, shi ma kuma mijin daga baya ya rasu kamar yadda sanarwar ta tabbatar, bayan ‘yan sanda sun kama shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
