Connect with us

News

Ba Za Ta Sabu A Sake Zabar Musulmai 2 A Kaduna Ba -SOKAPU

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kungiyar Kabilun Kudancin Jihar Kaduna (SOKAPU), ta ce a zaben 2023 sam ba za ta taba sabuwa a sake yin tsarin zabar musulmai biyu a matsayin gwamna da mataimaki ba.

Hukumomin tattara bayanan sirri sun ba ni kunya – Buhari

Advertisement

A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Luka Binnyiyat, ta fitar a jihar ta ce ba zasu sake marawa ‘yan addini daya baya ba.

 

Advertisement

Sanata Uba Sani, ya wallafa a shafinsa sada zumunta na facebook a ranar Litinin, na tabbatar da daukar Mataimakiyar Gwamna jihar mai ci a yanzu, Dakta Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyarsa.

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yi ammana da cewa, a bangarorin biyu na jihar akwai Kiristoci da Musulmai da suka cancanta wanda kuma suka fi dace wa a dauka a matsayin mataimaka a kowace jam’iyyar siyasa.

Advertisement

A cewar sanarwar gwamna El-rufai na sane da cewa yawan al’ummar da ke a kudancin kaduna ba su kai yawan adadin Kiristocin da ke a yankin ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Ba wai muna kin jinin Dakta Hadiza bane, amma ya kamata a yi adalci kuma sake daukarta a matsayin mataimakiya kamar cin fuska ne a gare mu.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending