News
Yau Kwankwaso zai gabatar da mataimakinsa Fasto Idahosa
Daga yasir sani Abdullah
A ranar Litinin din nan ne dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, zai gabatar da mataimakinsa ga ‘yan kasar.
Wasu hotuna da dan takarar ya wallafa a shafinsa na Facebook sun nuna tsohon gwamnan na Jihar Kano da tawagarsa suna duba babban dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja, inda za a gudanar da taron.
Nlc Zata Gudanar Da Zanga-Zanga A Dukkanin Najeriya Kan Dogon Yajin Aikin ASUU
A makon jiya ne Sanata Kwankwaso ya Fasto Idahosa, dan asalin Jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya, a matsayin mutumin da zai yi masa mataimaki a zaben 2023.
Faston, wanda fitaccen mawakin bushara ne, ya taɓa samun lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya a matsayin jakadan zaman lafiya, saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban bil adama da zaman lafiya ta hanyar wa’azinsa.
Ya fitar da kundi uku na jerin waƙoƙin bushara a baya.
Bishop Isaac Idahosa shi ne shugaba, kuma babban Fasto na cocin God First Ministry, wadda aka fi sani da Illumination Assembly, da ke Lekki Ajah, a jihar Legas.
Cocin da ya kafa sama da shekaru 25 da suka gabata.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
