Connect with us

News

Nlc Zata Gudanar Da Zanga-Zanga A Dukkanin Najeriya Kan Dogon Yajin Aikin ASUU

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC tace ranakun 26 da 27 zai zama ranakun da zasu gudanar da zanga-zanga a dukkanin fadin Najeriya, domin tilastawa Gwamnatin Tarayya, sa Kungiyar Malaman Jami’o’i su Tattaunawa kan matsalolin su, sannan su janye yajin aiki.

NDLEA ta kama wata mata za ta yi safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Oman

Advertisement

Kungiyar ASUU ta kulle dukkanin Jami’o’in Najeriya a ranar 14 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022, sakamakon kasawar Gwamnati na cika yarjejeniyar da suka tsara a shekaru da dama.

ASUU, da sauran Ƙungiyoyi na buƙatar ganin an bada isassun kuɗaɗe ga Jami’o’i na tafiyar dasu, da batun amincewa da manhajar biyan Albashi ta UTAS, gami da ƙarin girma da Albashi.

Idan za’a tuna NLC ta baiwa Gwamnatin Tarayya kwanaki 21 domin sasanta dukkanin abubuwa dake gabansu. Amma a halin yanzu wannan kwanakin sun ƙare domin magance ta.
Biyo bayan ƙarewar wa’adin, NLC a cikin wata sanarwa da Shugaban ta Ayuba Wabba ya fitar, yace zasu gudanar da zanga-zangar ban girma, zai gudana a faɗin Jahohi 36 da Abuja.

Sanarwar tace “akan yadda Majalisar Zartaswa na Kungiyar ta fitar a taron NEC na Kungiyar, daya gudana a ranar 30 ga watan yunin Shekarar 2022, mun yanke hukunci zamu maida yaran mu makaranta tare da goyon bayan Ƙungiyoyin Jami’o’i Makarantun Gwamnati domin samun ingantaccen ilmi

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending