Connect with us

News

Hisbah ta aske gashin ɗaliban da su kai askin banza don murnar yin kandi a Kano

Published

on

Hisbah

Daga kabiru basiru fulatan

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta kai wani sumame babbar Makarantar Sakandare ta Grammar da ke garin Dawakin inda ta kama wasu ɗalibai da askin banza a kansu, wai domin murnar kammala karatun sakandire.

Advertisement

Dakarun Hisbah ɗin sun yi nasarar damƙe da dama daga cikin ɗaliban, waɗanda su ka yi askin da a ke wa laƙabi da “ba kwaɓa”.

Bayan dakarun sun kama da na kama wa, wasu kuma sun tsere, sai su ka zaunar da su a harabar makarantar, inda su ka aske musu gashin tas.

Advertisement

Wannan na ƙunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da jami’in Sashen Fasahar Sadarwa ta Zamani na Hisbah din, Abdulwahab Said Ahmad, a shelkwatar ta da ke birnin Kano.

Ya ce an yi wa ɗaliban dake kammala jarrabawar gama sikandiren aski ne saboda wanda su ka yi a kawunansu ya saba da al’adar Hausawa da kuma tarbiyya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending