Connect with us

News

Gwamna Lalong ya nemi afuwa kan zarginsa da ‘saɓo’

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Gwamnan Filato, Simon Lalong ya nemi afuwan mabiyan cocin Katolika kan kalamansa da suka jawo ce-ce-ku-ce lokacin da ya ke kare matsayar nadin da jam’iyyarsa ta APC ta yi ma sa.

Advertisement

Tun a ranar Talata aka soma wata takaddama tsakanin Gwamnan jihar Filato Simon Lalong da Mabiya addinin Kirista ‘yan darikar Katolika.

Hakan ya biyo bayan kalaman da gwamnan ya yi cewa Fafaroma Francis bai ga laifin karbar mukamin darakta-janar na kamfe din ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, ba duk da cewa dukkansu Musulmai ne.

Advertisement

Kalaman sun fusata kiristoci mabiya katolika wadanda suka bayyana ambato sunan Fafaroma a zaman raini ga jagoran nasu.

Abin da ya kai ga sun bukaci a gaggauta dakatar da Lalong daga harkokin cocin.

Advertisement

Sai dai a wata wasika da ya aike wa cocin, Lalong ya amsa cewa ya yi kuskure don haka ya nemi a yafe ma sa, da alkawarta ci gaba da ayyukansa ta hanya mafi dacewa.

Gwamna Lalong ya ce bai yi wadannan kalamai ba domin muzanta kiristocin kasar

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending