Connect with us

News

NLC ta bukaci shugaba Buhari ya ruɓanya al’bashin ma’aikatan Najeriya

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Ƙungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta nemi gwamnatin Tarayya ta kara albashin ma’aikata da kashi 50 cikin 100 lura da yanayin tsadar rayuwa.

Advertisement

NLC ta mika wannan bukata ga shugaba Muhammadu Buhari ta wasikar da ke dauke da sa hannun shugabanta Ayuba Wabba.

Wasikar ta yi tuni da cewa gwamnonin su suka karfafa batun janye tallafin mai, da kawo batun ritayan ma’aikatan gwamnati a shekara 50, da kuma rage kudaden da ake bai wa majaliasa domin aikin mazabu.

Advertisement

Ƙungiyar ta caccaki gwamnoni kan wadannan shawarwari, su na mai cewa duk wanda ya goyi bayan ra’ayinsu to ba shi da maraba da makiyin gwamnati.

NLC ta ce batun karin albashi ne abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin a wannan lokaci shi ne mai muhimmanci.

Advertisement

Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace albashi da samawa ‘yan kasar sauki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending