News
Wike Bai Halarci Ganawar Atiku Da Yan Takarar Shugaban Ƙasa Ba
DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas bai halarci wani taro ba a ranar Laraba a lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da masu neman takarar shugabancin jam’iyyar a 2023 a gidansa da ke Asokoro a Abuja.
Baya ga Wike, akwai kuma tsoffin shugabannin majalisar dattawa Bukola Saraki da Pius Anyim da kuma gwamna Emmanuel Udom na jihar Akwa Ibom.
Kwamitin Tsare-tsaren Kuɗaɗe na CBN ya nuna damuwa kan hauhawar farashi da tsadar rayuwa a Najeriya
Sai dai wadanda suka halarci taron sun hada da Dele Momodu, Mohammed Hayatu-Deen, Tari Oliver, da Charles Ugwu.
Atiku ya yaba musu bisa yadda suka amince da sakamakon taron da ya haifar da shi a matsayin dan takarar PDP, da rashin tada kura.
Ya kuma yi alkawarin yin aiki da dukkan su gabanin zaben 2023, inda ya kara da cewa suna da rawar da za su taka domin samun nasarar sa a zaben.
Tun da farko Atiku ya gana da tawagar jihar Neja karkashin jagorancin tsohon ministan yada labarai Farfesa Jerry Gana.
A nasa jawabin, Gana ya ce sun kasance a gidan Atiku domin taya shi murna da kuma tabbatar masa da goyon bayansu da kuma jajircewa wajen ganin ya lashe jihar Neja.
Gana ya kuma bayyana cewa sulhun da ake yi tsakanin Atiku da Wike yana samun nasara.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa Wike ya karbi bakoncin abokinsa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a Ribas inda suka kaddamar da reshen jami’ar Emohua ta jihar Rivers dake karamar hukumar Emohua a jihar.
A zaben fidda gwanin da aka yi a watan Mayu, Atiku ya samu kuri’u 371 inda ya doke abokin hamayyarsa, Wike, wanda ya samu kuri’u 237.
Biyo bayan sakamakon zaben fidda gwanin da aka yi, Wike ya yi takun-saka da Atiku kan zaben Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa. Wike ya kuma bukaci shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu da ya yi murabus domin maye gurbinsa a kudancin kasar nan.
