Connect with us

News

Masar ta saki dan jaridar Al Jazeera da ta tsare

Published

on

Al Jazeera

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta bayyana cewa hukumomi a Masar sun saki dan jaridar ta Ahmed El-Nagdy da suka tsare.

Advertisement

 

Wannan na zuwa ne yayin da shugaban kasar ta Masar Abdel Fattah al-Sisi ke ziyara a Qatar – wurin da kafar yada labaran ke yada shirye-shiryenta.

Advertisement

 

Haka-zalika, wannan ne kuma karon farko kenan tun bayan da kasashen biyu suka dawo da huldar dangantaka a shekara da ta wuce bayan rashin jituwa ta diflomasiyya.

Advertisement

Kotun Jigawa Ta Yanke Wa Masu Fyade 4 Hukuncin Daurin Rai Da Rai

An tsare El-Nagdy tsawon shekara biyu, inda har yanzu ake ci gaba da tsare abokanan aikinsa biyu.

Advertisement

 

Gwamnatin Masar karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Sisi ta sha kama ‘yan jaridan Al Jazeera kan abin da ta kira na yada labaran da basu dace ba da take yi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending