Connect with us

News

Ƙungiyoyin fansho da na ƙwadago sun yi zanga-zanga a Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ƙungiyar ƴan fansho da hadin gwiwar kungiyar ƙwadago sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a jihar Kano, don nuna bacin ransu ga gwamnati saboda rashin biyansu hakkokinsu.

‘Yan kungiyar sun yi tattaki zuwa fadar gwamnatin jihar inda suka yi kira da jan hankali game da halin da suke ciki domin gwamnati ta dauki matakin gaggawa.

Advertisement

Mutum 30 Sun Nutse A Ruwa Yayin Tsere Wa ’Yan Bindiga A Zamfara

Gwamnati dai ta ce tana kokarin shawo kan matsalar nan da wani lokacin.

Advertisement

‘Yan fanshon wadanda suka nemi agajin kungiyar kwadago wajen matsa wa gwamnati lamba ta biya su kudaden fanshon da suke bi na tsawon lokaci, sun mika kokensu a rubuce.

Kwamared Kabiru Ado Minjibir shugaban kungiyar ƙwadago a jihar Kano ya ce kudaden barin aiki (gratuity) da suke bin gwamnati ya haura Naira biliyan 30.

Advertisement

Shugaban ma’aikata na Jihar ta Kano Alhaji Usman Bala shi ne ya karbi koken ‘yan fanshon a madadin gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Ya ce gwamnati tana sane da matsalolin da suke faruwa kuma sun fara daukar mataki a kai.

Advertisement

Bayanai na cewa ‘yan fansho a jihar sun jima suna fama da irin wadannan matsalolin tun daga lokacin da gwamnati ta kwashi kudadensu fiye da naira biliyan 20 aka gina gidaje da zummar samar musu da hanyoyin samun kudade.

Amma kuma ga alama har yanzu wannan dabarar ba ta haifar da abin da ake so ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending