Connect with us

News

NDLEA ta kama ɗan Nijar ɗaya da ‘yan Pakistan bisa zargin safarar koken

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun kama wani ɗan Nijar da ‘yan Pakistan biyu bisa zargin safarar koken.

Advertisement

Ganduje ba ya cikin gwamnonin da za su biya ma’aikata kuɗi hannu da dukiyar sata’

A sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an kama ‘yan Pakistan din a filin jirgin sama na Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, yayin da aka kama ɗan Nijar ɗin a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar

Advertisement

 

Hukumar ta ce ta kama ‘yan Pakistan ɗin – masu suna Asif Muhammed mai shekara 45, da kuma Hussain Naveed, mai shekara 57 – da laifin safarar koken da nauyinta ya kai kilo 2,985.5kg, a yayin da suke shirin hawa jirgi zuwa birnin Lahore na Pakistan.

Advertisement

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen na da takardun izinin zama a Najeriya, waɗanda take zargin cewa na bogi ne, kuma suna yawan zuwa Najeriya da nufin yin kasuwancin atamfofi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending