News
UNICEF ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta kuɓutar da yaran da aka sace a Katsina
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce dole gwamnatin tarayya ta dauki matakan da suka dace domin kuɓutar da yaran da aka sace a gona a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A makon da ya gabata ne dai ‘yan bindiga suka yi garkuwa da yara 21 waɗanda suka haɗa da ‘yan mata 17 da maza hudu a lokacin da suke aiki a wata gona a garin Mairuwa.
Nijeriya da Mexico sun ƙulla yarjejeniyar kasuwancin zoɓo
Rahotonni sun ce ‘yan bindigar sun ƙaddamar da harin ne, saboda mai gonar ya ƙi biyan harajin da ‘yan bindigar suka sanya wa manoman yankin.
A wata sanarwa da wakiliyar UNICEF a Najeriya Cristian Munduate ta fitar, ta bayyana damuwarta game da sace yaran, tana mai cewa bai kamata yara su zama abin harin ‘yan bindiga ba.
“UNICEFya damu matuƙa game da rahoton garkuwa da yara 21 da ke aiki a gona a garin Mairuwa, da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina”, in ji Cristian Munduate.
Ta ci gaba da cewa “Rahotonni sun tabbatar da sace yara 21, waɗanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 18”.
“Sace yara a gida, ko a makaranta, ko a gona, ko ma ina ne abin Allah wadai ne. Bai kamata yara su zama waɗanda rikici ke shafa ba, musamman ga wanda ya kamata ya kare su”, in ji Cristian.
Ta kuma yi kira gwamnati da ta kubutar da yaran tare da waɗanda aka sace su tare a gonar.
