News
An saka hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Tigray
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An kammala tattaunawa tsakanin manyan jami’an gwamnatin Habasha da takwarorinsu na yankin Tigray, inda suka saka hannu domin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Mun Shirya Dakile Sayen Kadarori Da Kudaden Haram-Cewar Hukumar EFCC
A yayin wani taron manema labarai a birnin Nairobi na ƙasar Kenya, duka ɓangarorin sun amince za a ci gaba da kai kayayyakin agaji ba tare da wata matsala ba a yankin na Tigray.
BBC ta rawaito cewa Akwai miliyoyin farar hula da ke buƙatar abinci da magunguna a ƙasar bayan shafe shekara biyu ana gwabza yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.
A halin yanzu dai ƙungiyoyin bayar da agaji na jiran umarni domin tura kayan agaji wuraren da ake buƙatarsu a yankin na Tigray.
Advertisements
