Connect with us

News

ICPC ta ƙwace gidaje 97, ta rufe asusun banki 1,233 na mutanen da ake zargi da rashawa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar yaƙi da ayyukan rashawa a Najeriya ta Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) ta ce ta ƙwace gidaje aƙalla 97 daga hannun mutane daban-daban cikin shekara huɗu da suka wuce.

Advertisement

 

Cikin jerin kadarorin da ta ƙwace akwai gine-gine 33, da filaye, da wata ma’aikata waɗanda hukumar ta ƙwace daga wajen Dr Jimoh Olatunde, tsohon akanta a hukumar shirya jarrabawa ta JAMB.

Advertisement

Kotu: Alhassan Doguwa ya nemi afuwar dan jarida bisa zargin cin zarafinsa

ICPC ta bayyana wa Jaridar Punch cewa ta kuma garƙame asusun ajiya 1,233 tun daga 2019 zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Advertisement

 

Bugu da ƙari, 60 daga cikin asusan mutanen da ake zargi da aikata rashawa, an miƙa su ga gwamnatin tarayya.

Advertisement

 

Asusan na ɗauke da kuɗi naira miliyan N547.7 da kuma dalar Amurka $669,248.89 jimilla.

Advertisement

 

Tsohon Gwamnan Zamfara Abdulazeez Yari na cikin waɗanda aka ƙwace wa kuɗin, inda gwamnati ta karɓe masa dala $669,248.89 da kuma naira N24,289,910.89.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending