News
Jam’iyyar APC Ta Lashe Dukkan Zaben Kananan Hukumomin Neja Yayin Da PDP Ta Kauracewa Zabe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi 25 a zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja ta gudanar a ranar Alhamis.
Kwamishinan ayyuka a hukumar Kwamared Ibrahim Aliyu Tunganwawa ne ya sanar da sakamakon a Minna.
Babu Binciken Zargin Safarar Kwayoyi Da Muke Kan Tinubu – INEC
Ya ce sakamakon wasu matsaloli hukumar za ta sake gudanar da zabe a unguwanni biyu na kananan hukumomin Rafi da Kontagora.Unguwannin biyu na Kusherki na Rafi ne da Tungan wanda aka fi sani da Kontagora aka sake yi a yau.
Kwamared Ibrahim Aliyu Tunganwawa wanda ya bayyana zaben da aka gudanar cikin lumana da kwanciyar hankali duk da wasu kananan matsaloli ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 13 ne suka halarci zaben kananan hukumomi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kauracewa shiga zaben ne domin kalubalantar tsarin zaben a kotu.
Idan dai za a iya tunawa, majalisar dokokin jihar ta kuma yi fatali da zaben a kan cewa jihar ba ta da kudi wajen samar da aikin a yanzu.
