News
Lawan Ya Sake Shan Kaye, Kotu Ta Tabbatar Da Machina A Matsayin Dan Takarar APC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukunci kan karar da jam’iyyar APC ta shigar kan dantalarar Sanatan Yobe ta Arewa. Kamar Radio Nageria Kaduna ta ruwaito
Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensen, wadda ta jagoranci wani kwamiti mai mutane 3, tabbtar da hukunci bayan da ta saurari mahawara daga bangarorin biyu da lamarin ya shafa.
Malaman addini a Sudan na zanga-zanga kan sabon kundin tsarin mulkin ƙasar
A karar, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan na kalubalantar hukuncin da mai shari’a Fadimatu Aminu ta babbar kotun tarayya da ke Damaturu, ta yanke a ranar 28 ga watan Satumba na wannan shekara, inda ta bayyana Bashir , Machina a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC a Yobe Ta Arewa.
Machina ya lashe zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta shirya a watan Mayun 2022, yayin da Lawan ya zabi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani da jam’iyyar APC ta shirya a watan Yuni.
Lawan ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na APC a hannun tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu.
Sai dai an nemi Machina da ya hakura da tikitin takarar da yasamu, amma ya dage cewa ba zai janye wa Shugaban Majalisar Dattawa ba.
A yayin da ake fuskantar cece-kuce, jam’iyyar APC ta mika sunan shugaban majalisar dattawa ga hukumar zabe mai zaman kanta a matsayin dan takararta na Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa.
Wanann ne yasa, Machina ya garzaya kotu domin neman hakkinsa.
Machina a cikin karar sa, ya bukaci kotun da ta bayyana shi a matsayin zababben dan takarar sanata na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Mai shari’a Fatimatu Aminu ta soke zaben fidda gwanin bayan fage da da aka yi wanda ya samar da Lawan a ranar 9 ga Yuni, 2022.
Sakamakon haka, alkalin kotun ta umarci APC da ta mika sunan Machina ga INEC a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani da aka gudanar a watan Mayu
